Fadan da babu ruwan ka: Farfesa Wole Soyinka ya kuma yin kaca-kaca da Obasanjo

Fadan da babu ruwan ka: Farfesa Wole Soyinka ya kuma yin kaca-kaca da Obasanjo

Farfesa Wole Soyinka yayi watsa-watsa da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Babban Farfesan na Ingilishi yayi wannan kira ne a wani sabon littafin sa da ya rubuta kwanan nan.

Fadan da babu ruwan ka: Farfesa Wole Soyinka ya kuma yin kaca-kaca da Obasanjo

Zan so mu raba gardama da tsohon Shugaban kasa Obasanjo - Soyinka

Babban Farfesan da ake ji da shi a fadin Duniya Wole Soyinka ya bayyana cewa Obasanjo bai san komai ba ya kuma nemi a ba shi dama su zauna da tsohon Shugaban kasar domin su raba gardama game da yadda yayi mulkin kasar.

KU KARANTA: Abin da ya sa Shugaban kasar Faransa ya je Legas

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Farfesan yayi kaca-kaca da Obasanjo yace tsohon Shugaban zai iya sukar Gwamnatin Buhari yadda ya ga dama amma idan ya isa ya zo su yi magana kan shekaru 8 din da yayi yana mulkin Najeriya.

Har wa yau Wole Soyinka bai kyale Obasanjo ba inda yayi kaca-kaca da maganar dakin karatun da tsohon Shugaban kasan ya gina a Jihar Ogun. Farfesan yace da kudin sata na dukiyar Gwamnati aka gina wannan katamfaren wuri.

Fitaccen Marubucin kuma Masani a harkar Turanci yace babu abin da Obasanjo yayi cikin shekarun da yayi yana mulki sai dai kuma ga shi yanzu bai da aiki sai sukar wasu masu mulkin kamar kace ya shuka wata tsiya ne a lokacin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel