Nigerian news All categories All tags
Abubuwan da su ka sa dole mu fice daga Jam’iyyar APC Inji Shehu Sani

Abubuwan da su ka sa dole mu fice daga Jam’iyyar APC Inji Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani yace lokaci yayi da za su bar Jam’iyyar APC mai mulki

- ‘Dan Majalisar dai ya zargi Shugaban kasa da rashin takawa El-Rufai burki

- Shehu Sani ya koka da yadda Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufai yake mulki

Mun samu labari cewa Fitaccen ‘Dan Majalisar APC mai mulki a Arewacin Najeriya watau Sanata Shehu Sani yace dole su bar Jam’iyyar domin babu wani dalilin cigaban su na zama a APC kamar wasu Bayin ‘Yan siyasa.

Bakin alkalami ya bushe: Babu abin da zai hana mu barin Jam’iyyar APC don mu ba Bayi bane – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani yace za su tattara su bar APC

A cewar Sanatan na Kaduna ta tsakiya, Adams Oshiomole ya zo Jam’iyyar a makare domin babu abin da zai canza a Jam’iyyar. Sanatan yayi hira da Jaridar Punch a Birnin Tarayya Abuja yace an gaza shawo kan rikicin APC.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban APC a Kaduna ya koma PDP

Sanatan na Kaduna yace har Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi sakaci wajen magance rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar inda ya gaza hana kama-karyar da Gwamna Nasir El-Rufai yake yi a Jihar Kaduna.

Shehu Sani ya koka da yadda Gwamnan ya rusa gidan ‘Dan Majalisar Dattawan da yayi kokarin ganin ya zama Gwamna a Jihar amma babu abin da Shugaban kasar yayi. Sani yace babu dalilin cigaba da zama a APC.

Sani ya bayyana cewa sau 3 ana kokarin sasanta su da Gwamnan inda Inuwa Abdulkadir ya fara kokarin haka. Daga baya dai Gwamna Aminu Masari da kuma Bola Tinubu sun yi kokarin sasanta su amma abin ya ci tura.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel