Nigerian news All categories All tags
Rikicin jihar Benuwe: Yansanda sun kama jami’an gwamnatin jihar dake kashe mutane

Rikicin jihar Benuwe: Yansanda sun kama jami’an gwamnatin jihar dake kashe mutane

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da cafke wasu gaggan yan bindiga guda Takwas dake da hannu cikin rikicin jihar Benuwe tayar da zauni tsaye, kamar yadda kamfani dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunayen yan bindigar kamar haka; Benjamin Tivfa mai shekara 32, Kansila daga mazabar Fidi cikin karamar hukumar Makurdi, Victor Ganabe, Daniel Kyase, guda cikin jami’an dake yaki da kiwon shanu a jihar, da kuma Julius Avaan.

KU KARANTA: Hattara dai! gwamnatin jihar Kaduna ta bullo da wata hanyar kawar da yan sara suka

Kaakakin rundunar Yansandan Najeriya,Jimoh Moshood ya bayana sauran yan bindigan sun hada da Terkula Udeh mai shekaru 37, Sunday Cheche 34, Alhaji Adajo Tomza shi ma jami’i dake yaki da kiwon shanu a jihar, da kuma Msugh Teraki mai shekaru 23.

Kaakakin ya sanar da haka ne a ranar Talata, 3 ga watan Yuni,a babban birnin tarayya Abuja, inda yace Yansanda sun samu nasarar kama yan miyagun mutanen ne a ranar 27 ga watan Yuni, inda suka kwato bindigu kirar AK 47 guda biyu, karamar bindiga daya, da kuma alburusai da dama.

Haka zalika shi wannan kansilan dake cikinsu, Benjamin Tivfa ya tabbatar da hannunsa cikin hare haren da ake kaiwa jihar Benuwe, sa’annan yace shike samar musu da makamai, da kuma kudi don gudun samun tsaiko a ayyukansu.

Daga karshe Jimoh yace har yanzu suna cigaba da gudanar da bincike don bankado duk wasu masu hannu cikin wannan lamari, don su fuskanci hukunci, inda yace za a gurfanar da mutanen gaban Kotu nan bada jimawa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel