Nigerian news All categories All tags
Shugaba Macron zai baiwa Najeriya tallafin kudi masu yawan gaske

Shugaba Macron zai baiwa Najeriya tallafin kudi masu yawan gaske

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gana da takwaransa na Najeriya shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi magana akan muhimman abubuwa da dama da suka hada da tattalin arziki da tsaro

Shugaba Macron zai baiwa Najeriya tallafin kudi masu yawan gaske

Shugaba Macron zai baiwa Najeriya tallafin kudi masu yawan gaske

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gana da takwaransa na Najeriya shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi magana akan muhimman abubuwa da dama da suka hada da tattalin arziki da tsaro.

DUBA WANNAN: An baiwa ministocin Birtaniya wasiyyar yanda zasu yi jana'izar Sarauniyar Ingila

Wannan shine karo na farko da Shugaba Macron ya kawo ziyara Najeriya a matsayin sa na shugaban kasa, shugaban yayi alkawarin bawa Najeriya tallafin Dalar Amurka miliyan 75 domin taimakawa matasa da aikin dogaro da kai.

Kasashen biyu sun cimma matsaya game da bashin dala miliyan 475 domin inganta harkokin sufuri a jihar Legas da kuma samar da ruwan sha a jihar Kano, yayinda kuma za'a bunkasa dajin dake jihar Ogun.

Kafin ya kawo ziyararsa Najeriya, shugaba Macron ya gana da shugabannin kasashen Afrika a taron da suka gudanar a Mauritania, taron da ya mayar da hankali akan sha'anin tsaro a kasashen dake yankin Sahel da suke fama da rikicin Boko Haram.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel