Zaben 2019: Mambobin PDP 500 sun sauya sheka zuwa APC a Lagas

Zaben 2019: Mambobin PDP 500 sun sauya sheka zuwa APC a Lagas

Akalla mutane 500 yan PDP ne suka sauya sheka a jihar Lagas a ranar Talata, 3 ga watan Yuli inda suka koma jam’iyyar APC.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa wadanda suka sauya sheka zuwa APC din sun bayyana kudirin nasu ne a wani babban taro da aka gudanar a sakatariyan APC dake Ikeja.

Masu sauya shekan daga uankuna 57 na jihar sun samu jagorancin tsohon jigon PDP, Mista Elijah Awodeyi.

Zaben 2019: Mambobin PDP 500 sun sauya sheka zuwa APC a Lagas

Zaben 2019: Mambobin PDP 500 sun sauya sheka zuwa APC a Lagas

Sun samu kyakyawan tarba daga sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar, Mista Tunde Balogun.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro zai zamo barazana ga zaben 2019 – Kungiyar CAN

Ya ce zuwan nasu na nufin sun bi jirgin APC sannan kuma cewa zasu kasance tare da jam’iyyar don ganin sun kawo cigaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel