Nesa ta zo kusa: A karo na farko Jihar Kano ta samu karuwa da jami’a mai zaman kanta

Nesa ta zo kusa: A karo na farko Jihar Kano ta samu karuwa da jami’a mai zaman kanta

Hukumar kula da jami’o’I ta kasa (NUC) ta bayar da lasisin fara aiki ga jami’a mai zaman kanta ta farko a jihar kano.

Sakataren NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, ne ya mika lasisin ga mai jami’ar, Kamal Puri, wani dan kasuwa daga kasar Indiya.

Jami’ar, Skyline University, it ace jami’a mai zaman kanta ta farko a jihar Kano kuma ta biyu a kaf yankin arewa maso yamma.

Nesa ta zo kusa: A karo na farko Jihar Kano ta samu karuwa da jami’a mai zaman kanta

A karo na farko Jihar Kano ta samu karuwa da jami’a mai zaman kanta

Jami’ar Al-Qalam ta jihar Katsina da aka bude a shekarar 2005 ita ce jami’a ta farko mai zaman kanta a yankin arewa maso yamma.

An fara bude jami’a mai zaman kanta a Najeriya a shekarar 1999.

A cewar Rasheed, jami’ar ta Skyline it ace jami’a ta 75 mai zaman kanta a Najeriya.

DUBA WANNAN: Gwanatin Kano da kasar China sun rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya, duba hotuna

Akwai jami’o’in gwamnatin tarayya 42 a Najeriya, 47 na jihohi yayin da kuma 75 masu zaman kansu ne. Muna da jimillar jami’o’I 164 kenan a Najeriya. Wasu zasu ga kamar sun yi yawa amma ga wadanda suke cikin tsarin sun san sun yi karanci,” a cewar farfesa Rasheed.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel