Nigerian news All categories All tags
Ya gudu ya bar matar shi na tsawon shekara 6, kotu zata yanke hukunci

Ya gudu ya bar matar shi na tsawon shekara 6, kotu zata yanke hukunci

A ranar talata ne wata yar kasuwa, mazauniyar garin Ibadan, Adenike Isola, ta sanar da babbar kotun jihar Oyo dake birnin Ibadan cewa mijin ta Oluwakunle, yayi watsi da al'amuran ta, tun da ya bar gidan su a ranar 19 ga watan Maris, 2012

Ya gudu ya bar matar shi na tsawon shekara 6 kotu zata yanke hukunci

Ya gudu ya bar matar shi na tsawon shekara 6 kotu zata yanke hukunci
Source: UGC

A ranar talata ne wata yar kasuwa, mazauniyar garin Ibadan, Adenike Isola, ta sanar da babbar kotun jihar Oyo dake birnin Ibadan cewa mijin ta Oluwakunle, yayi watsi da al'amuran ta, tun da ya bar gidan su a ranar 19 ga watan Maris, 2012.

Matar da lauyan ta Mista Kehinde Adegbite, ya jagoranta tace, ta gano mijin ta bashi da aikin yi tun bayan auren su a 2011.

DUBA WANNAN: Ruwa ya tafi da mutane 8 a jihar Niger

Tace Oluwakunle yayi mata karyar cewar yana aikin shirya wurin taro, inda daga baya ta gane bashi da aikin yi.

"Na zamanto ni kadai ke dawainiya da gidan tun 21 ga watan Afirilu, 2011. Mun yi aure a 21 ga watan Afirilu, 2011 kuma mun yi zaman aure dashi ne na wata 11. Inda ya tattara komatsan shi ya barni a ranar 19 ga watan Maris, 2012. "

Duk wani yunkurin nemo shi ya tashi a banza, tunda ko lambar wayar shi bata tafiya. Dole tana na tattara na bar gidan hayan da muke na lamba 56 Bashorun area dake Ibadan saboda karewar kudin hayan." inji ta

Lauyan ta ya roki kotun da ta yanke igiyar auren da ke tsakanin matar da mijin ta.

Adegbite yace doka ta bada damar rabuwa in har ma'aurata basa tare na shekara 3. Kuma wanda ake karar bai bayyana gaban kuliya ba, balle ya bada dalilan shi.

Bayan sauraren karar, mai shari'a E.O Ajayi ya dage sauraron karar zuwa 2 ga watan Octoba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel