Nigerian news All categories All tags
Wasu fusatattun 'Yan Najeriya sun bukaci Saraki da Dogara su ajiye mukaman su

Wasu fusatattun 'Yan Najeriya sun bukaci Saraki da Dogara su ajiye mukaman su

Daruruwan wadanda suka ki goyan baya a karkashin CATBAN sunyi kira ga shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara dasu sauka daga mukaman su

Wasu fusatattun matasa sun bukaci Saraki da Dogara su ajiye mukaman su

Wasu fusatattun matasa sun bukaci Saraki da Dogara su ajiye mukaman su

Daruruwan wadanda suka ki goyan baya a karkashin CATBAN sunyi kira ga shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara dasu sauka daga mukaman su.

Masu zanga zangar wadanda suka mamaye gidan gwamnatin tarayya akan ababan hawa suna dauke da tutoci wadanda suke nuni da fusata dangane da kundin tsarin mulkin kasar nan.

DUBA WANNAN: Shugaban kasar Faransa zai kai ziyara gidan Fela

Wanda ya hada wannan gangami Comrade Garba Wala a yayin da yake ganawa da manema labarai ya zargi masu yanke hukunci dayin amfani da kundin tsarin mulki wajen cin kudin Najeriya.

Wala yace duba da kasafin kudi na shekarar 2018 da shugaban kasa Muhammad Buhari ya gabatar ya bayyana cewa gidan gwamnatin tarayya suna "wawasar dukiyar al'umma ta hanyar kundin tsarin mulkin kasar nan. "

Gidan gwamnatin tarayya ta yanke biliyan 347 na kasafin 4,700 da aka kaddamar musu, inda suka gabatar da nasu kudirorin su na kansu 6,403 wanda yakai naira biliyan 578.

Yayi kira ga hukumar EFCC da ICPC da suyi bincike akan wannan lamari..

NAN ta rawaito cewa hakurin masu zanga zangar ya kare duba da kin cewa komai a garesu.

Wasu daga cikin su sunyi kokarin haura kofar gidan gwamnatin tarayya din yayin da wasu suke jijjiga kofar domin su samu hanyar shiga harabar wajen.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel