Nigerian news All categories All tags
Buhari ya sanya labule tare da shugaban kasar Faransa, an yi gemu da gemu

Buhari ya sanya labule tare da shugaban kasar Faransa, an yi gemu da gemu

A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da takwaransa na kasar Faransa sun sanya labule yayin da suka shiga wata ganawar sirri a fadar gwamnatin Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labaru,NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da misalin karfe 4:35 na ranar Talata ne shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya isa fadar shugaban kasa, inda shugaba Buhari da kansa ya tarbe shi.

KU KARANTA: Buhari zai kai ziyara wata jihar a yankin Arewa maso gabashin Najeriya

Buhari ya sanya labule tare da shugaban kasar Faransa, an yi gemu da gemu

Ana jiran Buhari da Macron

Daga cikin wadanda suka raka ma Buhari baya akwai gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun tare da ministoci da wasu daga cikin hadiman shugaba Buhari, haka zalika ana sa ran tattaunawa tsakanin Buhari da Macron zai ta’allaka ne akan tsaro da ta’addanci.

Idan za’a tuna a ranar Litinin, 2 ga watan Yuli ne shugaba Buhari ya gana da Macron a yayin taron kungiyar kasashen Afirka da ya gudana a kasar Mauritania.

Bayan ganawa da Buhari, Macron zai wuce jihar Legas don kai ziyara gidan fitaccen mawakin nan Fela Anikulapo Kuti, wanda akafi sani da suna Fela, da kuma gidan rawarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel