Nigerian news All categories All tags
Masu zanga-zanga sun mamaye majalisa: Mun san masu daukan nauyinsu – Sanatoci

Masu zanga-zanga sun mamaye majalisa: Mun san masu daukan nauyinsu – Sanatoci

A yau, Talata, ne wasu matasa karkashin wata kungiya mai rajin ceto Najeriya daga hannun balagurbin shugabanni (CATBAN) ta fara gudanar da wata zanga-zanga a gaban zauren majalisar tarayya.

Saidai Sanatocin Najeriya sun bayyana masu zanga-zangar a matsayin makiya cigaba da kuma dimokradiyya.

Masu zanga-zangar sun mamaye kofar shiga zauren majalisar inda suke kira ga shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da takwaransa na majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da su gaggauta yin murabus daga kujerunsu.

Masu zanga-zanga sun mamaye majalisa: Mun san masu daukan nauyinsu – Sanatoci

Masu zanga-zanga sun mamaye majalisa

Jagoran masu zanga-zangar, Ibraheem Wala, ya bayyana cewar shugabannin majalisun biyu; Saraki da Dogara, basu da tarbiyar day a kamata a ce suna rike da kowanne irin mukami a kasar nan.

A jawabinsa, mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, ya bayyana kungiyar CATBAN a matsayin ‘yan kwangilar zanga-zanga tare da bayyana cewar matasan sun mayar da hakan hanyar samun kudi.

DUBA WANNAN: 2019: Dole a samu dan takara daga jihohin nan na arewa 3 idan ana son kayar da Buhari - Kwankwaso

A nasa bangaren, Sanata Isa Hamma Misau, ya bayyan cewar wani daga cikin ministocin shugaba Buhari ne ya dauki nauyin shirya zanga-zangar. Saidai bai ambaci suna ba.

Saraki, a jawabinsa ya bayyana cewar masu daukar nauyin zanga-zangar suna cikin gwamnati tare da jaddada muhimmanci ilimintar da ‘yan Najeriya a kan muhimmanci da amfanin kudin da ake warewa ‘yan majalisa domin gudanar da aiyuka a mazabunsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel