Nigerian news All categories All tags
Aradu ta halaka wani dalibin jami’a har lahira

Aradu ta halaka wani dalibin jami’a har lahira

Wani dalibin jami’ar jihar Anambra, dan aji daya mai suna Vincent Uche Mbanefo ya gamu da ajalinsa a ranar Talata, bayan da Aradu ta fado masa yayin da yake dakinsa bayan wani mamakon ruwan sama da ya sauka, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Wani dalibin jami’an ya tabbatar ma majiyar Legit.ng da mtuuwar Uche, inda yace sun gano gawarsa ne a dakinsa bayan wani lokaci da gama ruwan, suka tarar da gawarsa ta yi baki kirin! Sai dai yace sun yi mamakin saukar aradun, sakamakon ruwan da aka yi ba mai karfi bane.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan bindiga sun bude ma jami’an Yansanda wuta a Abuja, sun kashe 7

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Mohammed Haruna ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace an garzaya da Uche zuwa Asibiti don ceton rayuwarsa, amma a Asibitin ne ma likitoci suka tabbatar da mutuwar tasa.

Aradu ta halaka wani dalibin jami’a har lahira

Aradu

“Mun sanar da iyayen Uche game da mutuwarsa, kuma tuni aka mika gawarsa zuwa kauyensu dake Aguleri don binnne shi.” Inji Kaakaki Muhammed Haruna.

A wani labarin kuma, wani matashi mai shekaru Arba’in ya kashe kansa a karamar hukumar Arewacin idemili na jihar Anambra, ta hanyar rataye wuyansa da igiya a jikin wata fankar sama dake dakinsa a ranar Talata da misalin karfe hudu na rana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel