Nigerian news All categories All tags
Buhari zai kai ziyara wata jiha a yankin Arewa maso gabashin Najeriya

Buhari zai kai ziyara wata jiha a yankin Arewa maso gabashin Najeriya

Shirye shirye sun yi nisa don tarbar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin ziyarar da zai kai jihar Borno a ranar Juma’a, 6 ga watan Yuli, kamar yadda kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ne ya sanar da haka a ranar Talata, 3 ga watan Yuli a fadar gwamnati dake babban birnin tarayya Abuja, bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhamamdu Buhari.

KU KARANTA: Fulani makiyaya sun ci wasu Inyamurai taran naira miliyan 2 saboda kashe musu shanu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Shettima ma cewa ya kai ziyarar fadar shugaban kasa ne don bayyana ma shugaba Buhari irin shirin da suke yi don bashi kyakkyawar tarba a ziyarar da zai kai jihar Borno a ranar Juma’a mai zuwa.

Haka zalika gwamnan ya bada tabbacin an kusan kawo karshen rikicin yan ta’addan Boko Haram, inda yace: “Yaki da ta’addanci ya kusan zuwa karshe, mai yiwuwa ne akwai yan matsaloli kadan, amma idan aka yi duba da halin da muke ciki a shekaru hudu da suka gabata da yanzu, za’a ga cewa an samu sauki sosai.” Inji shi.

A wani labarin kuma, tsohon ministan ma’danan kasa, kuma dan takarar gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya yi wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda suka kwashe sama da mintuna Talatin suna tattauna batun zaben gwamnan jihar da za’a yi a ranar 14 ga watan Yuli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel