Nigerian news All categories All tags
Buhari ya aika wasika ga majalisar dattijai, ya nemi izinin yin sabon nadi

Buhari ya aika wasika ga majalisar dattijai, ya nemi izinin yin sabon nadi

- Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wasika zuwa ga majalisa game da sabuwar nadi a CBN

- Shugaba Buhari ya nada Folashodun Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan CBN

- Shugaban kasan yana bukatar majalisar dattawa ta amince da nadin Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin kasar

Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wasika ga majalisar dattawa inda ya ke bukatar su amince da nadin Folashodun Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin kasa wato CBN.

Premium Times ta ruwaito shugaba Buhari ya zabi Shonubi don cike wannan matsayin.

Shugabab majalisa Bukola Saraki ne ya karanto wasikar shugaba Buhari bayan sunyi wata ganawar sirri na sa'a daya a yayin dawo zaman majalisar a ranar 3 ga watan Yuli.

Buhari zaiyi sabuwar nadi a CBN, ya aike wa majalisa da wasika

Buhari zaiyi sabuwar nadi a CBN, ya aike wa majalisa da wasika

KU KARANTA: Kashe-kashen Filato: Anyi zanga-zangar neman kama T.Y Danjuma da Jona Jang a Hedikwatar 'Yan Sanda dake Abuja (hotuna)

A cikin wasikar shugaban kasar ya bukaci majalisar ta tantance Folashodun Adebisi Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan CBN kamar yadda sashi na 81(2) na dokar babban bankin Najeriya (CBN) na 2007 ta tanadar.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ajiye aiki na mataimakin gwamnan CBN mai kula da sashin ayyuka, Adebayo Adelabu, daga ranar 15 ga watan Yulin 2018.

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da takardan murabus din da Adelabu ya aike dashi a ranar 24 ga watan Mayu.

Shugaban kasan ya yiwa Adelabu godiya bisa ayyukan da ya yiwa wa kasarsa Najeriya kuma ya masa fatan alkhairi a duk abubuwan da zaiyi a gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel