Nigerian news All categories All tags
Kisan jigo a jam'iyyar APC: 'Yan sanda sun kama mutane 5, duba sunayensu

Kisan jigo a jam'iyyar APC: 'Yan sanda sun kama mutane 5, duba sunayensu

Jami'an Yan sanda na musamman masu yaki da fashi da makami FSARS na Jihar Imo sunyi nasarar kama mutane biyar da ke da hannu cikin kashe jigo a jam'iyyar APC na jihar, Amos Akano.

An sace Akano ne gab da za'ayi babban taron kasa na jam'iyyar APC kuma daga bisani aka samu rahotton tsintar gawarsa kwanaki kadan bayan taron.

Punch ta ruwaito cewa jami'an FSARS karkashin jagorancin kwamandansu Godfrey Victor sun kai simame yayinda masu garkuwa da mutanen suke jirar a kawo musu kudin fansa kafin su saki marigayin.

An kama mutum 5 dake da hannu cikin kashe jigon jam'iyyar APC a Imo, duba sunayensu

An kama mutum 5 dake da hannu cikin kashe jigon jam'iyyar APC a Imo, duba sunayensu

KU KARANTA: Badakallar $40m: EFCC tayi nasara a kan dan uwan Jonathan

A cewar kwamishinan Yan sanda na jihar, Dasuki Galadanci, an damke wandanda ake zargin ne a Ihiala dake jihar Anambra.

Kwamishinan ya bayyana sunayensu kamar haka: Ikenna Nwosu wanda akafi sani d Ezego da Chibuike Martins da Emeka Eke da Chijioke Akukara da Adubuokwu Chibueze, ya kuma ce suna fashi ne a jihohin Anambra da Imo.

Galadanci ya ce kama wandanda ake zargi din babban nasara ce ga yaki da masu aikata miyagun ayyuka da ma kiyaye afkuwar miyagun ayyuka a jihar.

A sanarwan da ya bayar, kwamishinan yan sandan ya ce, "A baya yan kungiyar suna buya ne a Mgbidi a karamar hukumar Oru ta jihar Imo suna jiran a iyalan mamacin su kawo musu kudin fansa ne lokacin da yan sandan suka kama su a Ihiala a jihar Anambra.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel