Shari'ar Metuh: Kotu ta bayar da umurnin gurfanar da lauyansa da 'yan jarida uku

Shari'ar Metuh: Kotu ta bayar da umurnin gurfanar da lauyansa da 'yan jarida uku

Babban kotun Abuja ta bayar da umurnin a gurfanar da wani lauya dake zaune a Abuja, Ben Chuks Nwosu tare da wasu ma'aikatan gidan talabijin na Channels bisa zarginsu da laifin cin zarafin kotu.

A yau Talata ne Justice Abang ya umurci Attorney Janar na kasa (AGF) Abubakar Malami (SAN) ya kuma gurfanar da masu gabatar da shirin 'Sunrise' a gidan talabijin na Channels; Chamberlain Usoh, Gimba Umar da kuma wani guda daya domin a tabbatar idan ya dace su rika tattauna shar'iar dake gaban kotu a shirinsu.

Shari'ar Metuh: Kotu ta bayar da umurnin gurfanar da lauyansa da 'yan jarida uku

Shari'ar Metuh: Kotu ta bayar da umurnin gurfanar da lauyansa da 'yan jarida uku

KU KARANTA: Badakallar $40m: EFCC tayi nasara a kan dan uwan Jonathan

Nwosu, daya daga cikin lauyoyin da suke kare tsohon mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Olisa Metuh ya hallarci shirin a ranar 22 ga watan Mayu inda ya yi magana akan rashin amincewa Metuh ya fita kasar waje neman lafiya da kotu tayi.

"Akwai abubuwan da ba kowa ya sani ba game da shari'ar Metuh, suna son a musgunawa Metuh ne kuma a jefa shi a kurkuku kuma hakan ba dai-dai bane," Inji Nwosu kamar yadda alkali ya umurci nuna masa faifan muryar a kotu.

Sai dai alkalin bai bayar da umurnin a gurfanar da lauyan EFCC, Johnson Ojogbane ba saboda ba'a iya gano ko shi wanene ba daga muryarsa a hirar da aka dauka a faifan rediyo.

A yayin da yake yanke hukunci a kan bukatar Metuh na bude shari'arsa domin ya kare kansa wanda aka riga aka rufe bayan ya ki hallartar kotun, Alkalin ya ce kotun ba zata iya komawa kan wannan shari'ar ba sai dai ya daukaka karar a wata kotun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel