Zanga-zangar yan sanda: Gwamnan Borno na ganawar sirri da Kyari

Zanga-zangar yan sanda: Gwamnan Borno na ganawar sirri da Kyari

Kasa da sa’o’i ashirin da hudu bayan wasu jami’an yan sanda da aka tura jihar Borno sun gudanar da zanga-zanga, a yanzu haka Gwamna Kashim Shetima na wata ganawar sirri da shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Abba Kyari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ku tuna cewa an aika sammaci ga Sufeto Janar na yan sanda, Ibrahim Idris yan sa’o’i kadan bayan zanga-zangan yan sandan sannan an gano shi a ofishin shugaban ma’aikata.

Sai dai ba’a bayyana ba ko fadar shugaban kasa ta sammace shi ne don yayi bayanin dalilin da ya sa jami’an suka yin zanga-zanga.

KU KARANTA KUMA: Buhari yafi kaunar Najeriya fiye da kansa - Gwamna Ganduje Buhari yafi kaunar Najeriya fiye da kansa - Gwamna Ganduje

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Wani jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party,PDP, a jihar Akwa Ibom, Sanata Anietie Okon ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus daga matsayinsa saboda gazawar shugabancinsa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a a kasar.

Sanata Okon wanda yayi magana da manema labarai a Uyo, ya koka kan yadda gwamnatin dake mulki ke tafiyar da lamarin tsaro a yankunan kasar, musamman a jihohin Plateau da Benue duk da al'umma na kokawa kan waannan matsalar dake afkuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel