Nigerian news All categories All tags
nPDP: Mun yanke shawarar cigaba da kasancewa a jam'iyyar APC - Senata Na'Allah

nPDP: Mun yanke shawarar cigaba da kasancewa a jam'iyyar APC - Senata Na'Allah

Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Bala Na'Allah (APC, Kebbi) ya ce shugabanin sabuwar PDP sun yanke shawarar cigaba da zama a jam'iyyar APC.

Na'Allah wanda aka ambata sunansa a cikin mambobin sabuwar jam'iyyar PDP da suka komo jam'iyyar APC gabanin zaben 2015 ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa baza su fice daga APC ba.

nPDP: Mun yanke shawarar cigaba da kasancewa a jam'iyyar APC - Senata Na'Allah

nPDP: Mun yanke shawarar cigaba da kasancewa a jam'iyyar APC - Senata Na'Allah

"A jihar mu ta Kebbi, mun riga mun yanke shawara. Jihar mu jihar APC ce, gwamnan mu shima dan APC ne. Idan ina son sauya sheka zuwa wata jam'iyyar, babu wanda ke da ikon hana ni amma a yanzu ina nan a APC. Mutane sun dena yada karairayi game da ni," inji shi.

Ya kuma yi tsokaci game da abubuwan da suka tattauna game da nPDP da kuma irin rawar da tsohon ciyaman din jam'iyyar APC, John Odigie-Oyegun ya taka.

A baya, mambobin nPDP din sunyi barazanar ficewa daga jam'iyyar APC din muddin ba'a biya musu wasu bukatu da suke so ba, sun kuma yi ikirarin cewa jam'iyyar APC ta juya musu baya duk da irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar jam'iyyar a zaben 2015.

Ku biyo mu don samun karin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel