Nigerian news All categories All tags
Buhari yafi kaunar Najeriya fiye da kansa - Gwamna Ganduje

Buhari yafi kaunar Najeriya fiye da kansa - Gwamna Ganduje

- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ce shugaba Muhammadu Buhari sadaukin dan kishin kasa ne

- Ganduje ya kuma bayyana cewa shugaba Buhari ya fi son Najeriye fiye da kansa

- Ya ce shugaban kasa ya dukufa wajen kawo cigaba mai dorewa a Najeriya

A jiya Litinin ne Gwamna jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari sadauki ne wanda ya fi kaunar Najeriya fiye da kansa.

Premium Times ta ruwaito cewa gwamnan kuma ya ce Buhari mutum ne mai gaskiya da nagarta kuma ya kara da cewa: "Shi shugaba ne mai gaskiya kuma ya dukufa wajen gudanar da aikinsa."

Buhari yafi kaunar Najeriya fiye da kansa - Gwamna Ganduje

Buhari yafi kaunar Najeriya fiye da kansa - Gwamna Ganduje

KU KARANTA: Badakallar $40m: EFCC tayi nasara a kan dan uwan Jonathan

Ganduje ya yi wannan maganar ne a liyafar cin abinci na APC reshen Kudu maso gabashin Najeriya da akayi a Owerri babban birnin jihar Imo kamar yadda babban jami'in hulda da kafafen yada labaransa, Abba Anwar ya sanar a safiyar Talata 3 ga watan Yuli.

Ga wani bangare cikin sanarwan: "Shugaba Buhari alama ce ta hadin kai. Buhari yana kaunar Najeriya fiye da kansa. Ya dukkufa ne wajen ganin cewa an samu cigaba mai dorewa a Najeriya. Wannan liyafar cin abincin da akayi na karrama shi ya yi dai-dai," kamar yadda aka ruwaito gwamnan ya fadi.

Ganduje ya kuma yabawa APC reshen kudu maso gabashin Najeriya bisa shirya liyafar da kuma rally na hadin kai saboda Buhari. Ya kuma taya dukkan wanda su kayi nasarar samun mukamai a gangamin taron APC da akayi a cikin kwanakin nan.

A bangarensa, gwamna Okorocha ya yabawa jihar Kano saboda itace jihar Arewa da tafi yin maraba da yan kabilar Igbo fiye sa sauran jihohin Najeriya

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel