Nigerian news All categories All tags
Sanata ya bukaci Buhari da yayi murabus kan yawan kashe-kashe da ake yi

Sanata ya bukaci Buhari da yayi murabus kan yawan kashe-kashe da ake yi

Wani jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party,PDP, a jihar Akwa Ibom, Sanata Anietie Okon ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus daga matsayinsa saboda gazawar shugabancinsa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a a kasar.

Sanata Okon wanda yayi magana da manema labarai a Uyo, ya koka kan yadda gwamnatin dake mulki ke tafiyar da lamarin tsaro a yankunan kasar, musamman a jihohin Plateau da Benue duk da al'umma na kokawa kan waannan matsalar dake afkuwa.

Sanata Okon yace akwai bukatar jam'iyya mai mulki ta nusar da shugaban kasar sannan ta yi mai bayani a yaren da zai fahimtar da shi cewa sake fasalin lamuran kasar ne kadai mafita ga Najeriya.

Sanata ya bukaci Buhari da yayi murabus kan yawan kashe-kashe da ake yi

Sanata ya bukaci Buhari da yayi murabus kan yawan kashe-kashe da ake yi

Ya kuma nuna kokwato kan ko za'a iya gudanar da zabe a karkashin halin da tsaron kasar ke ciki, wanda a cewarsa hakan na cigaba da tabarbarewa a kullun.

KU KARANTA KUMA: Hadimin Buhari ya daura laifin rashin tsaro da kashe-kashe akan yan siyasa

Kan zargin da wasu jiga-jigan APC ke yi na cewa jam'iyyar PDP ce ke assasa kashe-kashen makiyaya karkashin gwamnatin Buhari, Okon ya ce, "Akwai abun da bazasu iya ganin laifin PDP ba?

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel