Badakallar $40m: EFCC tayi nasara a kan dan uwan Jonathan

Badakallar $40m: EFCC tayi nasara a kan dan uwan Jonathan

A jiya Litinin 2 ga watan Yuli ne babban kotun Legas tayi watsi da karar da dan uwan tsohon shugaban kasa Jonathan ya shigar inda ya ke zargin hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa EFCC ta keta masa hakkinsa na dan kansa.

Alkalin kotun, Mojisola Olatroegun ya ce karar a Robert Azibaola ya shigar bata lokacin kotu ne saboda ya shigar da irin wannan karar a wasu kotuna daban-daban.

A cewar Alkalin, hukumar EFCC ta bi dukkan dokokin da dokar kasa ta shimfida wajen gudanar da bincikensu a kan Mr. Azibaola.

Zargin damfara ta $40m: EFCC tayi nasara a kan dan uwan Jonathan

Zargin damfara ta $40m: EFCC tayi nasara a kan dan uwan Jonathan

Mr. Azibaola ya shigar da EFCC kara a kotun ne inda ya ke korafi a kan tsare shi da hukumar tayi bisa zarginsa da damfara na zunzurutun kudi $40 miliyan.

KU KARANTA: Kashe-kashen Filato: Anyi zanga-zangar neman kama T.Y Danjuma da Jona Jang a Hedikwatar 'Yan Sanda dake Abuja (hotuna)

Mr. Azibola ya yi ikirarin cewa hukumar EFCC na bincikarsa ne saboda alakarsa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan domin suna son ya fadi shafawa Jonathan laifi ta kowanne hali.

Kamar yadda a bayyana a wata takarda da ya shigar a kotu, Mr. Azibola ya ce tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro marigayi Patrick Andrew Azazi ne ya tuntube shi a shekarar 2012 inda ya bukaci ya taimaka masa wajen magance fashe-fashen bututun man fetur a yankin Neja - Delta.

Daga baya a watan Satumban 2014, an biya $40 miliyan cikin asusun ajiyar banki na kamfanin Oneplus Holdings Nigeria Ltd saboda aikin tsaron matatun man fetur din inda aka amince za'a biya shi 10% na kudin a matsayin la'adarsa.

Sai dai bayan an samu canjin gwamnati a Mayun 2015, an kafa kwamitin bincike don bibiyar kwangilayen da gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta yi hakan ne yasa aka umurci Oneplus Holdings ta dawo da $40 miliyan da aka bata a baya.

Hakan yasa aka kama Mr. Azibaola kuma aka tsare shi bayan samun izini daga wata kotun majistare bisa zarginsa da laifin almubazaranci da kudin al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel