Yanzu Yanzu: Buhari ya dawo Abuja bayan taron AU (hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja, babban birnin tarayyar kasar bayan kammata taron kungiyar kasashen Afirka a kasar Mauritania.
A yayin wannan taro na yini biyu, shugaban kasar ya bukaci kasashen Afirka da su taimaka ma Najeriya wajen dawo da kudaden kasar Najeriya da manyan barayin kasar suka boye a kasashensu.
KU KARANTA KUMA: Duk wani dan takara na PDP zai iya kayar da Buhari – Turaki
Ga karin hotuna daga dawowar nasa:
A ranar Litinin, 2 ga watan Yuli, Buhari ya gana da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron da ya halarci taron a matsayin bako, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin Afirka tare da sauran shuwagabannin kasashen nahiyar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng