Duk wani dan takara na PDP zai iya kayar da Buhari – Turaki

Duk wani dan takara na PDP zai iya kayar da Buhari – Turaki

Wani tsohon ministan ayyuka na musamman kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashin lemar PDP, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki yace ko wani dan takara dake neman takara karkashin jam’iyyar ya isa ya kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari idan har aka basa tikitin takara.

Turaki, babban lauyan Najeriya ya bayyana hakan a jiya a Abuja lokacin da ya ziyarci sakatariyar PDP na kasa don sanar da kwamitin jam’iyyar kudirinsa na son yin takara a jam’iyyar.

Tsohon ministan yace Najeriya bata taba rabuwa kamar na yanzu ba, inda ya kara da cewa yan kasa sun shiga motar halaka a 2015.

Duk wani dan takara na PDP zai iya kayar da Buhari – Turaki

Duk wani dan takara na PDP zai iya kayar da Buhari – Turaki

A cewarsa, “dukkanin yan takaranmu sun cancanci shugabancin kasar nan sannan dukkaninmu zamu yi gwaninta fiye da wanda Buhari ke yi a yanzu,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Mai ba Shugaba Buhari shawara tayi kaca-kaca da kungiyar CAN

Turaki ya ce shi baya siyasar ko a mutu, inda ya kara da cewa koda bai samu tikitin takara ba zai marawa duk wanda ya yi nasara a cikinsu.

Ya ce gwamnati mai ci bata amu ko wani dan PDP da laifin da za’a hukunta sub a tsawon shekaru uku, in ba tsoffin gwamnonin Plateau da Taraba ba, Joshua Dariye da Jolly Nyame, wanda yace an shirya shari’ansu ne a lokacin gwamnatin PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Online view pixel