Nigerian news All categories All tags
Bata-gari ne ke neman a tsige Hafsun Sojoji kuma duk inda mu ka ga dama za mu yi kiwo – Miyetti Allah

Bata-gari ne ke neman a tsige Hafsun Sojoji kuma duk inda mu ka ga dama za mu yi kiwo – Miyetti Allah

Kungiyar Miyetti Allah Kautal sun bayyana cewa duk mai kiran a tsige Hafsun Sojojin Kasar nan bata-gari ne. Sakataren Kungiyar ta Makiyaya Saleh Al-Hassan ne ya bayyana wannan.

Labari ya zo mana cewa ‘Yan kungiyar Miyetti Allah Kautal sun yaba da aikin da Shugabannin Sojojijn Kasar su ke yi na kawo karshen rikici a Najeriya. Makiyayan su kace ana bakin kokari wajen karbe makamai daga Miyagu

Bata-gari ne ke neman a tsige Hafsun Sojoji kuma duk inda mu ka ga dama za mu yi kiwo – Miyetti Allah

'Yan Miyetti Allah sun ce ba su neman tashin hankali a Najeriya

The Punch ta rahoto cewa Shugabannin Kungiyar Makiyaya Fulani ba su goyi bayan kiran da ake yi na tsige Shugabannin Hafsun Sojoji. Sakatare Janar na Kungiyar Miyetti Allah Kautal Saleh Al-Hassan ya bayyana wannan a wata hira.

KU KARANTA: Gowon ya nemi Shugaba Buhari ya kawo karshen kashe-kashe

Miyetti Allah tace a Kudancin Kaduna an kashe masu mutane kusan 411 amma ba su nemi ramuwa ba don a zauna lafiya a kasar. Al-Hassan ya nemi a kyale su su cigaba da kiwon dabbobin su cikin zaman lafiya ba tare da tsangwama da matsin lamba ba.

Sakataren Kungiyar ta Makiyayan na Najeriya yace tsarin da Kungiyar ECOWAS ta kawo ya ba Makiyaya dama su yi kiwo a duk inda su ka ga dama a Afrika. S. Al-Hassan yace haka-zalika babu ruwan su da kan iyakan kasashe da Turawan Mallaka su ka kirkira.

Saleh Al-Hassan ya bayyana cewa masu neman a cire manyan Sojojin kasar dai rubabbun ‘Yan siyasa ne ko kuma masu yi masu mugun aiki a boye. Fadar Shugaban kasa dai tace akwai hannun ‘yan siyasa dama a rikicin da ke aukuwa a cikin fadin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel