Nigerian news All categories All tags
Ana tunani ‘Yan wasan Super Eagles za su gana da Buhari a Fadar Aso Villa

Ana tunani ‘Yan wasan Super Eagles za su gana da Buhari a Fadar Aso Villa

Bisa dukkan alamu ‘Yan kwallon Najeriya na Super Eagles za su hadu da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa na Aso Villa bayan da aka fatattako kasar daga Gasar cin kofin na Duniya da ake bugawa a Kasar Rasha.

Ana tunani ‘Yan wasan Super Eagles za su gana da Buhari a Fadar Aso Villa

Buhari zao hadu da 'Yan kwallon Super Eagles idan ya dawo gida

Jaridar The Nation tace akwai kishin-kishin din cewa Shugaban kasar zai hadu da ‘Yan kwallon Najeriya da kuma maso horas da su a Ranar Laraba. Shugaba Buhari zai shirya walima da ‘Yan wasan da su ka wakilci kasar a Gasar Duniya.

Kafin a fara Gasar na kwallon kafa na Duniya, Shugaba Buhari ya hadu da ‘Yan wasan na Super Eagles inda har kyaftin din Kungiyar ‘Dan wasa John Mikel Obi yayi alkawarin dawowa gida da kofin. Sai dai tun a zagayen farko aka kori Najeriya.

KU KARANTA: An sace Mahaifin Kyaftin din 'Yan kwallon Najeriya

Wata majiyar tace an ga Mai kula da ‘Yan wasan Kasar watau Gernot Rohr a Garin Legas kuma da alamu Kungiyar kwallon kafan Kasar na NFF ba su da niyyar yi wa ‘Yan kwallon kasar wata tarba ta musamman bayan Najeriya ta dawo gida.

Babban ‘Dan wasan Najeriya Ahmed Musa ya samu tarba mai kyau bayan da ya iso Najeriya saboda kokarin da yayi a Rasha. Yanzu dai mun ji cewa har Najeriya ta fara shiryawa Gasar cin kofin Nahiyar Afrika da za a buga badi a kasar Kamaru.

Shugaban kasa Buhari zai hadu da 'Yan kwallon Super Eagles idan ya dawo gida Najeriya a Ranar Laraba. Shugaban kasar yayi 'yan kwanaki ba ya gida bayan da ya tafi taron kasashen Afrika a Mauritania.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel