Mai martaba ya sha kasa a Jihar Kwara bayan Alkali ya sauke sa

Mai martaba ya sha kasa a Jihar Kwara bayan Alkali ya sauke sa

Mun samu labari daga wasu jaridun kasar nan cewa wata Kotu da ke Garin Ilorin a Jihar Kwara ta tsige wani mai sarauta a Jihar inda tace babu shi babu rawani.

Mai martaba ya sha kasa a Jihar Kwara bayan Alkali ya sauke sa

Mai girma Gwamnan Jihar Kwara Abdulfatahi Ahmed

Wani Babban Kotun Tarayya da ke babban Birnin Ilorin na Jihar Kwara ta sauke Dr. Stephen Olajide daga sarauatar sa na Ollola Olla na Kasar Isin. Yanzu dai an sauke Mai martaba Olajide daga karagar mulki.

Kwanakin baya ne wanda ke rike da sarautar Aro na Olla watau Cif Adebayo Adeniyi ya ruga Kotu domin a dakatar da shirin nada Stephen Olajide a matsayin Ollola na Olla na kasar ta Isin da ke cikin Jihar Kwara.

KU KARANTA: An kama wani 'Dan Sanda yayi ksan kai a Najeriya

Cif Adebayo Adeniyi da wasu mutum 3 da ke neman sarautar sun shigar da karar ne a tsakiyar Watan jiya kuma yanzi Alkali ya yanke hukunci ya nemi a dakatar da nadin. Yanzu dai Kotu ta cirewa Olajide rawanin na sa.

Alkali mai shari’a M. Abdul Gafar ne ya yanke wannan hukunci bayan ya duba shari’ar da aka kawo masa. Mutane da dama dai na neman wannan sarauta inda yanzu Alkali ya amsa bukatar masu nema a dakata da nadin.

A can kwanakin baya ‘Dan tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido ya rasa sarautar sa. An tsige Mustafa Lamido ne daga Hakimin Garin Bamaina da ke Karamar Hukumar Birnin Kudu saboda yana neman ya shiga siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel