Nigerian news All categories All tags
PDP ta bukaci gwamnati ta bayyanawa jama'a abinda yasa bata biyan 'yan sanda hakkin su

PDP ta bukaci gwamnati ta bayyanawa jama'a abinda yasa bata biyan 'yan sanda hakkin su

Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci da a gabatar da kwakkwaran bincike akan zanga - zangar da jami'an 'yan sanda suka yi a jihar Borno, dake nuni da ba a biyan su hakkin su

PDP ta bukaci gwamnati ta bayyanawa jama'a abinda yasa bata biyan 'yan sanda hakkin su

PDP ta bukaci gwamnati ta bayyanawa jama'a abinda yasa bata biyan 'yan sanda hakkin su

Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci da a gabatar da kwakkwaran bincike akan zanga - zangar da jami'an 'yan sanda suka yi a jihar Borno, dake nuni da ba a biyan su hakkin su.

Jam'iyyar ta yi kiran ne a wata sanarwa da Sakataren jam'iyyar na yada labarai ya fitar, Mista Kola Ologbondiyan, a a jiya Litinin a babban birnin tarayya.

DUBA WANNAN: Ruwa ya tafi da mutane 8 a jihar Niger

Jam'iyyar ta nuna jimamin ta akan lamarin, inda take nuna cewar bai kamata ace abu irin wannan yana faruwa ba a jihohi da ake rikici irin wadannan, saboda jami'an sun bayar da rayukan su domin tsare na al'umma amma kuma ace har yanzu suna kuka da rashin basu hakkunan su.

Jam'iyyar ta ce idan har ba'a biyan su hakkin su, to dole baza su dinga gabatar da ayyukan su yanda ya kamata ba, kuma bai ma kamata ace su suna daji suna aiki ba, sannan kuma manyan su suna Ofis suna cinye kudi.

"Saboda haka muna bukatar a gabatar da kwakkwaran bincike akan lamarin nan, sannan kuma muna bukatar a bayyanawa al'umma domin su san gaskiyar abinda ke faruwa."

Sannan jam'iyyar ta bukaci jami'an 'yan sandan da suyi haquri. A karshe kuma ta bukaci gwamnati data yi kokari domin ganin ta biya jami'an hakkin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel