Oby Ezekwesili za ta maka Gwamnatin Tarayya a Kotu domin neman hakkin ta

Oby Ezekwesili za ta maka Gwamnatin Tarayya a Kotu domin neman hakkin ta

Mun samu labari cewa tsohuwar Ministar ilmin kasar nan Madam Oby Ezekwesili tana shirin shiga Kotu da Gwamnatin Tarayyar Najeriya a kan irin abin da ya faru da ita kwanakin baya a fadar Shugaban kasa.

Oby Ezekwesili za ta maka Gwamnatin Tarayya a Kotu
Ezekwesili na shirin zuwa kotu saboda an toye mata hakkin ta

Ministar ilmin Kasar nan a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo watau Oby Ezekwesili ta bayyana cewa za ta iya shiga Kotu da Gwamnatin Najeriya bayan an hana ta kutsawa wasu wurare a fadar Shugaban kasa.

A makon jiya ne tsohuwar Ministar da Tawagar ta su kayi kokarin shiga har fadar Shugaban kasa domin su kai kukan su. Sai dai Jami’an tsaro sun takawa Oby Ezekwesili da Jama’an na ta na Kungiyar ‘Red Card’ burki wanda bai mata dadi ba.

KU KARANTA: An kama Ma'aikacin gidan yari yana fashi

A lokacin da Shugabar Kungiyar ta BBOG ta shiga wata kasuwa a Jihar Legas jiyan nan ta bayyana cewa Gwamnatin kasar ba ta isa ta hana su neman hakkin su ba. Madam Oby Ezekwesili tace ba kuma za ta daga kafa a wajen fafatukar da ta ke yi ba

Tsohuwar Ministar dai tace idan ma ta kama su shiga Kotu da Gwamnatin kasar domin nemawa kan su hakki za su yi domin ganin an kawo gyara a sha’anin shugabancin Najeriyar. Ta kara da cewa da PDP da APC dai duk jirgi daya ya dauko su.

Jiya kun ji cewa Fadar Shugaban kasa ta nemi ta ga Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya a gaban ta bayan Jami’an tsaro sun yi zanga-zanga a Garin Maiduguri saboda rashin albashi da wasu alawus.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel