Nigerian news All categories All tags
An bankado wasu masu shirye-shiryen dakatar da shugaba Buhari takara saboda tsufansa

An bankado wasu masu shirye-shiryen dakatar da shugaba Buhari takara saboda tsufansa

- Da yiwuwar shugaba Buhari ya fuskanci matsala a takararsa ta 2019

- Wasu gungun manyan lauyoyi ne suke saka zaren hana shi takar

- Dama dai wasu sun dade da ganin baiken shugaban yunkurin sake tsayawa takara a 2019

A wani Rahoto da Jaridar The Nation ta wallafa a jiya ta bayyana yadda aka gano wata makarkashiya da aka shiryawa shugaban kasa Muhammadu Buhari domin hana shi sake yin takara, bisa yawan shekarunsu.

An bankado wasu masu shirye-shiryen dakatar da shugaba Buhari takara saboda tsufansa

An bankado wasu masu shirye-shiryen dakatar da shugaba Buhari takara saboda tsufansa

Wata Majiya daga fadar shugaban kasa wacce kuma ta bukaci da a sakaye sunanta ta bayyana yadda wasu manyan lauyoyi suka shirya tsaf domin kalubalantar shugaban kasa Buhari akan yunkurinsa na sake yin takara a shekarar 2019.

Lauyoyin masu lambar kwarewa ta SAN sun shirya gabatar da korafe-korafensu na ganin sun hana shugaban takarar da ya himmatu, cikin hujjojinsu akwai bukatar a hana dukka nin wani dan kasar nan da ya kai shekaru 70 rike wani ofishin gwamnati.

KU KARANTA: Labari mai dadi: An soma samar da tashar jirgin ruwa a yankin Arewa

Majiyar ta kara da cewa lauyoyin suna samun goyon bayan wasu masu adawa da sake tsayawar shugaba Buhari takara a Shekarar 2019, inda su ke daukar nauyinsu duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar nan bai haramtawa masu shekarun da su ka kai 70 neman wani matsayi ba. wanda hakan ke nuni da abin da lauyoyin su ke bai wuce mafarki ba.

Majiyar ta ce idanuwanta suna kan masu wannan yunkurin, wanda Babban burinsu shi ne su samu abin duniya ba.

A karshe sanarwar ta bukaci lauyoyin da su je su sake karanta sashi na 130 da 131 da kuma sashi na 137 na kundin tsarin mulkin kasar nan wanda aka yiwa kwaskwarima a shekarar 1999, wanda ya fayyace wanda ya cancanta ya tsayai takarar shugabancin kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel