Nigerian news All categories All tags
Sojojin sun damke wasu mutane 21 masu hannu a hare-haren da ake kaiwa Filato

Sojojin sun damke wasu mutane 21 masu hannu a hare-haren da ake kaiwa Filato

- Asirin masu tayar da hankali a jihar Filato ya fara tonuwa

- Yanzu haka an cafke mutane 21 tare da makamansu da suke kai hari

Kimanin mutane 21 ne hadakar rundunar tsaro ta sojoji na musamman su ka damke wadanda ake zargin suna da hannu a rikicin jihar Filato.

Wadanda suka shiga hannun jami'an tsaron an same su dauke da muggan makamai, wanda ake amfani da su wajen kashe-kashe a fadin jihar.

Sojojin sun damke wasu mutane 21 masu hannu a hare-haren da ake kaiwa Filato

Sojojin sun damke wasu mutane 21 masu hannu a hare-haren da ake kaiwa Filato

Hadakar rundunar tsaron sun hadar da jami'an yan sanda, sojin sama da dakarun sojojin kasa, da kuma sauran jami'an tsaro.

Tun da farko dai an yi holar wadanda ake zargin da aikata wannan laifi a ofishin rundunar hadakar jami'an tsaron da ke Jos.

Da suke karin bayani shugaban rundunar hadakar tsaron ta musamman Manjo Adam Umar da kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa reshen jihar Filato Tyopev Terna sun bayyana cewa cikin mutane 21 da aka damke, mutum 11 suna da alaka da kashe-kashen da aka yi a karamar hukumar Barkin Ladi da kewayenta, yayin da sauran mutum 14 su ke da alaka da rura wutar rikicin bayan lafawarsa.

KU KARANTA: An tsinci gawawwaki 23 a dajin Zamfara – Rahoto

Sun bayyana cewa bayanan da suka samu ne a wajen wani guda da suka kama kan rikicin da ya afku a yankin na Barikin Ladi, ya sanya nan ta ke su ka cafke wadanda ake zargi da aikata Laifin. Wanda hakan yana cikin kokarinsu na kawo karshen dukkanin masu hannu rikicin jihar Filato.

Wadanda aka damke din an same su da makamai kirar gida, da sauran muggan makamai. sannan kuma mafi yawa daga cikinsu akwai jini a jikin kayan da su ke sanye da su, an kuma samu guda daga cikinsu yana sanye da wando mai launin kakin sojoji.

Amma sai dai ba su bayyana sunayen mutane 21 wadanda ake zargi da hannu a cikin kashe-kashen ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel