Nigerian news All categories All tags
Hatsaniya ta barke a garin Pankshin lokacin da Jami'an hukumar NDLEA su ke kokarin Cafke wani dillalin Kwaya

Hatsaniya ta barke a garin Pankshin lokacin da Jami'an hukumar NDLEA su ke kokarin Cafke wani dillalin Kwaya

- NDLEA sun harbi iska a garin Pankshin yayin kama wani gwaskan mai siyar da kwaya

- Harbin ya afku ne yayin da mutane ke tsaka da cin kasuwa

- Sai dai kuma abin takaici shi ne gwaskan ya sulale ya tsere

An samu hatsaniya a garin Pankshin da ke jihar Filato lokacin da rundunar masu yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato NDLEA su ka fara harbin kan mai uwa da wabi a cikin kasuwar garin, lokacin da kasuwar ke tsaka da ci, a bisa yunkurin su na cafke wani dillalin kayan maye.

Hatsaniya ta barke a garin Pankshin lokacin da Jami'an hukumar NDLEA su ke kokarin Cafke wani dillalin Kwaya

Hatsaniya ta barke a garin Pankshin lokacin da Jami'an hukumar NDLEA su ke kokarin Cafke wani dillalin Kwaya

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito yadda jami'an suka dinga yin harbi a cikin kasuwar ta Pankshin, wanda ya haifar da samun raunika da kuma asarar dukiya.

Duk da irin wannan harbi da jami'an su kayi hakan bai sa sun yi nasarar damke wannan dillalin ba, sakamakon layar zana da yayi.

KU KARANTA: An samu gawar mutane 10 rataye a wani gida, ana binciken musababbin mutuwar su

Wata mata wacce al'amarin ya faru akan idonta mai suna Sara, ta bayyanawa manema labarai yadda jami'an NDLEA din suka biyo dillalin kayan mayen, inda shi kuma ya shigo kasuwar a lokacin da take tsaka da ci domin neman mafaka.

Shi ma wani da yake bayar da shaidar gani da ido mai suna John Danjuma ya bayyana yadda lamarin ya haifar da hatsari, wanda da ba don kiyayewar Ubangiji to babu shakka da an samu hasarar rayukan al'umma a yunkurinsu na tsira da rayukansu.

Da ya ke tofa Albarkacin bakin sa akan faruwar lamarin shugaban riko na Karamar hukumar Pankshin Mista Naomi Golmwen ya bayyana takaicinsa akan faruwar lamarin, Domin lamarin ya haifar da hatsaniya a cikin Kasuwar Garin.

A karshe ya shawarci jami'an hukumar ta NDLEA da su dinga gudanar da aikinsu bisa doka da tsari, domin gujewa afkuwar hakan a nan Gaba.

Da ya ke mayar da martani akan faruwar lamarin jami'in Hulda da Jama'a na rundunar ta NDLEA Mr Mathias Tyopev, Ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda kuma ya bukaci mutane su kwantar da hankalinsu, kuma su cigaba da al'amuransu yadda su ka Saba. Ya kuma kara da cewa Dukkanin wadanda su ka samu raunika hukumar ta su ta Kai su Babban Asibitin Pankshin inda su ke karbar magana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel