Nigerian news All categories All tags
Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mahaifin Mikel Obi

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mahaifin Mikel Obi

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun sanar da ceto mahaifin dan wasan Super Eagles Mikel Obi daga hannun miyagun mutane masu garkuwa da mutane a ranar Litinin, 2 ga watan Yuli, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, SP Ebere Amaraizu ya bayyana cewar sun samu nasara ceto Dattijo Michael Obi ne da misalin karfe 2:30 na rana, tare da direbansa mai suna Ishaya John, a karshen wani kungurmin Daji, mai suna Dajin Udi dake jihar Enugu.

KU KARANTA: Buhari ya karkare ziyarar kasar Mauritania ya kamo hanyar dawo gida

“Mun samu labarin an sace Dattijo Michael Obi tare da direbansa ne a ranar 29 ga watan Yuni akan hanyarsa Makurdi zuwa Enugu bayan ya fito daga garin Jos, inda aka neme su sama ko kasa aka rasa. Bayan wani dan lokaci sai yan bindigar suka fara kiran iyalansa a waya, suna neman kudin fansa miliyan goma.

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mahaifin Mikel Obi

Mahaifin Mike Obi

“Sai dai samun labarin garkuwar ke da wuya, sai jami’anmu suka dukufa don ganin sun ceto wannan bawan Allah, a dalilin haka an yi musayar wuta tsakanin Yansanda da barayin, da wuta yayi zafi sai barayin suka jefar da Dattijon, sa’annan suke ranta ana kare.” Inji shi.

Da yake jawabi, majiyar Legit.ng ta ruwaito mahaifin Mikel Obi ya yaba ma Yansanda tare da mika godiyarsa garesu, inda yace: “Nagode ma Yansanda, na tsira da raina, kuma ina cikin koshin lafiya, Nagode ma kwamishinan Yansanda da jami’ansa.”

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mahaifin Mikel Obi

Mahaifin Mikel

Daga karshe Kaakakin ya bukaci ma’aikatan asibitocin garin da su taimaka ma Yansanda da rahotanni game da duk wani mutumi da ya je asibiti a ciwon harbin bindiga, sa’annan ya jaddada manufar Yansanda na kawo karshe ayyukan barayin mutane a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel