Buhari ya karkare ziyarar kasar Mauritania ya kamo hanyar dawo gida

Buhari ya karkare ziyarar kasar Mauritania ya kamo hanyar dawo gida

A yayin da aka karkare taron kungiyar kasashen Afirka a kasar Mauritania, shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu halartar taron ya nufo gida Najeriya don cigaba da tafiyar da kasar, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.

A yayin wannan taro na yini biyu, Buhari ya roki kasashen Afirka da su taimaka ma Najeriya wajen dawo da kudaden kasar Najeriya da manyan barayin kasar suka boye a kasashensu.

KU KARANTA: Yabon gwani ya zam dole: Tambuwal ya baiwa Shehu Abdullahi kyautar gida, fili da kujerar Makka

Buhari ya karkare ziyarar kasar Mauritania ya kamo hanyar dawo gida

Buhari

Haka zalika shima shugaban kasar Mauritania, Mohammd Ould Abdel Aziz ya bayyana shugabankasa Muhammadu Buhari a matsayin jigon nahiyar Afirka, inda yace da ace Afirka kasace guda, da Buhari ne shugabanta.

Haka zalika a ranar Litinin, 2 ga watan Yuli, Buhari ya gana da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron da ya halarci taron a matsayin bako, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin Afirka tare da sauran shuwagabannin kasashen nahiyar.

Buhari ya karkare ziyarar kasar Mauritania ya kamo hanyar dawo gida

Buhari

Buhari ya samu rakiyar gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, na jihar Nassarawa, Tanko Almakura, ministan Ilimi, Adamu Adamu da kuma ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama.

Buhari ya karkare ziyarar kasar Mauritania ya kamo hanyar dawo gida

Buhari

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel