Nigerian news All categories All tags
Yabon gwani ya zam dole: Tambuwal ya baiwa Shehu Abdullahi kyautar gida, fili da kujerar Makka

Yabon gwani ya zam dole: Tambuwal ya baiwa Shehu Abdullahi kyautar gida, fili da kujerar Makka

Gwamnatin jihar Sakkwato ta karrama dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, wato Super Eagles, Shehu Abdullahi da kyaututtuka don nuna farin cikinsu da rawar da ya taka gasar cin kofin Duniya, inda ya wakilci Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal ne ya sanar da kyatuttukan ga Shehu a yayin wani taron karramawa da aka shiya masa a fadar gwamnatin jihar, inda yace sun bashi kyautar katafaren gida mai dakuna hudu da kujerar Makkah.

KU KARANTA: Yadda Sojojin Najeriya suka halaka yan Boko Haram 5 a wasu kauyukan Borno

Yabon gwani ya zam dole: Tambuwal ya baiwa Shehu Abdullahi kyautar gida, fili da kujerar Makka

Tambuwal da Shehu

Haka zalika gwamna Tambuwal ya umarci kwamishinan sifiyo da ya nemi dandadeshen fili ya baiwa Shehun don ya cika burinsa na gina katafaren cibiyar wasanni a jihar. Gwamnan ya kara da yin kira ga matasan Sakkwato da su jajirce kamar Shehu Abdullahi, kuma su guji shaye shaye da bangar siyasa.

Shima a jawabinsa, Shehu ya bayyana godiyarsa ga gwamnan jihar game da wannan karramawa da aka yi masa a gida, sa’annan ya yaba masa bisa kokarin da ya keyi na ganin ya ciyar da al’amuran wasanni gaba, tare da yaki da shaye shayen miyagun kwayoyi.

Yabon gwani ya zam dole: Tambuwal ya baiwa Shehu Abdullahi kyautar gida, fili da kujerar Makka

Shehu da Tambuwal

Daga karshe Shehu ya dauki alkawarin gina cibiyar wasanni a jihar tare da taimakon masu hannu da shuni a jihar, sa’annan ya mika ma gwamnan kyautar rigar kwallon Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel