Nigerian news All categories All tags
Manyan ‘Yan Majalisar APC a Jihar Oyo za su bi Jam’iyyar ADC

Manyan ‘Yan Majalisar APC a Jihar Oyo za su bi Jam’iyyar ADC

Tun ba yau ba dai an dade ana rikicin cikin gida a Jam’iyyar APC a Jihar Oyo. Dazu mu ka samu labari cewa wasu ‘Yan bangaren na Jam’iyyar APC a Jihar sauya sheka zuwa Jam’iyyar ADC.

Manema labarai a Najeriya sun tabbatar da cewa wasu ‘Yan Taware a Jam’iyyar APC mai mulki da ke karkashin Unity Forum a Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya sun tattara kayan su sun koma Jam’iyyar adawa ta ADC.

Manyan ‘Yan Majalisar APC a Jihar Oyo za su bi Jam’iyyar ADC

Jam'iyyar APC a tayi wani gagarumin rashi Jihar Oyo

Wasiu Olatunbosun, wanda shi ne Shugaban wadannan ‘Yan taware kafin ficewar su daga APC yayi magana da ‘Yan jarida dazu a Garin Ibadan inda ya bayyana cewa shi da wasu ‘Yan Majalisa kusan 14 na Jihar sun barJam'iyyar ta APC.

Mista Olatunbosun ya kuma bayyanawa ‘Yan jarida cewa bayan nan akwai Sanatoci 2 cikin 3 na Jam’iyyar da su ka sauya shekan. Daga cikin wadanda su ka bar Jam’iyyar APC har da Mataimakin Kakakin Majalisar dokokin Jihar.

KU KAEANTA: Sufeta Janar na 'Yan Sanda ya amsa kira a fadar Shugaban kasa

Jagoran ‘Yan tawaren watau Olatunbosun yace Gwamna Abiola Ajimobi ba yayi da su don haka su ka bar Jam’iyyar. Akwai akalla manyan APC 2000 da kuma Magoya bayan su sama da mutum 100, 000 da za su bi sahu wajen komawa Jam’iyya ADC.

Kwanan nan ne dai Jam’iyyar adawar ta ADC ta bi tafiyar tsohon Shugaban kasa Obasanjo. Tsohon Shugaban kasar dai ya dage wajen kokarin ganin Shugaban kasa Buhari ya sha kashi a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel