Nigerian news All categories All tags
Janar Gowon yayi magana game da kashe-kashen da ake yi a mulkin Buhari

Janar Gowon yayi magana game da kashe-kashen da ake yi a mulkin Buhari

Mun samu labari cewa tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wani abu game da kashe-kashen da ake yi a kasar nan. Gowon yace addu’a ce za ta ceci kasar nan.

Janar Gowon yayi magana game da kashe-kashen da ake yi a mulkin Buhari

Gowon ya nemi Shugaba Buhari ya kawo karshen rikicin Filato

The Nation ta rahoto cewa Janar Yakubu Gowon yayi kira Shugaban kasa Buhari ya gano masu kashe Bayin Allah a Najeriya ya hukunta su. Janar Gowon ya kuma nemi Gwamnatin Tarayya ta sakawa wadanda rikicin ya auka masu.

Tsohon Shugaban kasar wanda yayi mulki a lokacin da Najeriya ke yakin basasa ya nemi a hukunta wadanda ke tada rikici a kasar. Kashe-kashen da ake yi a kasar dai ya ki ci ya kuma ki cinyewa a lokacin Shugaban kasa Buhari.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta kara yin wani babban rashi a Jihar Kaduna

Janar Yakubu Gowon mai ritaya yake cewa nufin Ubangiji ne kurum Najeriya ta zauna lafiya amma ba don ikon Allah ba da tun tuni kasar ta wargaje. Janar Gowon (rtd) yayi wannan jawabi ne a Jihar Katsina wajen wani taro yau.

Kwanan nan ne aka shirya wani taro a kan harkar tsaro a Arewa maso Yammacin Kasar. Tsohon Shugaban ya soki masu kokarin raba kan ‘Yan kasar da kalaman kiyayya inda ya nemi ‘Yan kasar su cigaba da addu’ar zaman lafiya.

Kwanaki Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya tofa albarkacin su game da rikicin Filato inda aka kashe mutane da dama a Garin Jos. Obasanjo ya nemi a kawo karshen wannan rikici.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel