Nigerian news All categories All tags
Kudin kamfen na PDP: EFCC ta koma Borno, ta gurfanar da tsohon minister Wakil da sayransu kan N341m

Kudin kamfen na PDP: EFCC ta koma Borno, ta gurfanar da tsohon minister Wakil da sayransu kan N341m

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC a ranar Litinin, 2 ga watan Yuli ta gurfanar da wani tsohon karamin ministan wutar lantarki, Muhammad Wakil da wasu mutane hudu a gaban Justis M.T Salihu na babban kotun tarayya dake Maiduguri, jihar Borno bisa zargin zambar kudi na sama da naira miliyan 341.

Sauran wadanda aka gurfanar tare da shi sun hada da, Garba Abacha, Ibrahim Shehu Birma, Dr. Abubakar Ali Kullima da kuma Engr. Muhammad Baba Kachalla.

Ana zargin Wakil da sauran masu laifin kan zargin karban kudi dala miliyan 115 wanda tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke ta sace domin makomar zaben shugabancin kasa na 2015.

Kudin kamfen na PDP: EFCC ta koma Borno, ta gurfanar da tsohon minister Wakil da sayransu kan N341m

Kudin kamfen na PDP: EFCC ta koma Borno, ta gurfanar da tsohon minister Wakil da sayransu kan N341m

Wadanda ake karar basu amsa laifinsu ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Katagum

Mashawarcin lauyan, H.A Shehu ya sanya ranar shari’a, yayinda ya bukaci kotu da ta tsare wadanda ake kara a kurkuku.

Mai shari’an Justis Salihu ya dage lamarin zuwa ranar 3 ga watan Yuli don jin kaídar belin sannan yayi umurnin su cigaba da kasancewa a hannun EFCC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel