Nigerian news All categories All tags
Gwamna Fayose ya rasa manyan ‘Yan PDP har 400 a Jihar Ekiti

Gwamna Fayose ya rasa manyan ‘Yan PDP har 400 a Jihar Ekiti

- Wasu da ke tare da Jam’iyyar PDP a da sun koma APC

- Hakan na iya kawowa Gwamna Ayo Fayose cikas a zabe

- Ayodele Fayose yana shirin barin gadon kujerar Gwamna

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Ekiti mai shirin barin gado Ayodele Peter Fayose da Jam’iyyar sa ta PDP sun yi babban rashi daf da zaben da za ayi a Jihar na sabon Gwamna kwanan nan.

Gwamna Fayose ya rasa manyan ‘Yan PDP har 400 a Jihar Ekiti

Wasu da ke tare da Fayose sun koma goyon bayan Fayemi

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Jam’iyyar ta PDP mai mulki a Jihar Ekiti ta rasa manyan ‘Ya ‘yan ta kusan 400 a Jihar inda su kace za su yi wa Minista Kayode Fayemi na Jam’iyyar APC aiki a zabe mai zuwa da za ayi.

KU KARANTA: Shugaban Gambiya ya tsige Mataimakiyar sa daga mulki

Manyan ‘Yan PDP da ke tare da Prince Adedayo Adeyeye karkashin tafiyar Kungiyar PAAM sun tattara sun bar Jam’iyyar ta PDP. Wadanda su ka sauya shekan sun fito ne daga Yankin Eyio, Esure da kuma Irapora da ke Jihar Ekiti.

Tsofaffin ‘Yan Jam’iyyar ta PDP sun bayyana cewa sun bi ‘Dan takarar APC Kayode Fayemi ne saboda mutum ne mai kima da mutunci da kuma dattaku. Wadanda su ka sauya shekar dai sun gargadi INEC ta guji murde zaben da za ayi.

Kwanaki kun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da zaben 2014 da Ayo Fayose yayi nasara yana mai nuna takaicin sa da abin da ya faru a lokacin zaben. Shugaban kasar yayi nemi APC tayi bakin-kokari ta a zaben bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel