Nigerian news All categories All tags
Ta hada baki da mahaifiyarta sun kashe mahaifinta

Ta hada baki da mahaifiyarta sun kashe mahaifinta

A yau dinnan ne babbar kotun birnin tarayya ta Apo, ta bayyana cewar wata yarinya data hada baki da mahaifiyarta suka kashe mahaifinta, inda a yanzu haka ake tsare dasu a gidan kurkuku na Suleja

Ta hada baki da mahaifiyarta sun kashe mahaifinta

Ta hada baki da mahaifiyarta sun kashe mahaifinta

A yau dinnan ne babbar kotun birnin tarayya ta Apo, ta bayyana cewar wata yarinya data hada baki da mahaifiyarta suka kashe mahaifinta, inda a yanzu haka ake tsare dasu a gidan kurkuku na Suleja.

Mai shari'a Idris Kutigi, ya bada umarnin tsare yarinyar, Kusha Kure da mahaifiyarta Asabe, wadanda aka kama su da hannu dumu - dumu a lamarin.

DUBA WANNAN: Mai horas da 'yan wasan Super Eagles zai ajiye aikin sa

Daga baya alkalin ya daga cigaba da sauraran karar har zuwa 19 ga watan September.

Wani dan sanda ya bayyanawa kotu cewar sun aikata laifin nasu ne a ranar 10 ga watan Mayun wannan shekarar.

Yace da 'ya da uwar duka suna sayar da itace ne a kauyen Karavan dake Bwari, babban birnin tarayya, inda suka hada baki suka kashe mahaifin nata mai suna Kure a ranar 10 ga watan Mayu.

A bayanin shi ya bayyanawa kotu cewar yarinyar tayi korafin cewar mahaifin nata yaki goya mata baya ne akan auren wani saurayinta da take so mai shekaru 24.

Laifin ya sabawa sashe na 97 da kuma sashe na 221 na dokar kasa. Sannan kuma hada baki wurin aikata kisa hukuncin sa kisa ne a sashe na 221 na dokar kasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel