Nigerian news All categories All tags
Kotu ta bayar da umarnin a tsare tsohon minista Muhammed Wakil bayan EFCC ta gurfanar da shi a yau

Kotu ta bayar da umarnin a tsare tsohon minista Muhammed Wakil bayan EFCC ta gurfanar da shi a yau

A yau, Litinin, hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon ministan wutar lantarki, Muhammad Wakil, da wasu mutane 4 gaban mai shari’a M.T Salihu na babbar kotun tarayya dake Maiguduri bisa tuhumarsu da badakalar kudi, miliyan N341m.

Ragowar mutanen su ne Garba Abacha, Ibrahim Birma, Abubakar Kullima da Muhammad Kachalla.

Ana tuhumar Mista Wakil da ragowar mutane hudu da karbar dalar Amurka $115 daga tsohuwar minister man fetur, Diezani Alison-Madueke, domin yakin neman zaben shugaban kasa na 2015.

Kotu ta bayar da umarnin a tsare tsohon minista Muhammed Wakil bayan EFCC ta gurfanar da shi a yau

Jami'an hukumar EFCC

Dukkan wadanda ake tuhuma sun ki amsa laifinsu.

DUBA WANNAN: Ka manta da cin zabe don ko mazabarka ba zaka ci ba – Ganduje ya mayarwa Kwankwaso martini

Lauyan hukumar EFCC, H. A. Shehu ya nemi kotu ta bayar da umarnin tsare wadanda ake zargin a gidan yari. Bukatar da lauyan wadanda ake tuhuma, M. Umoru, ya gaggauta sukanta tare da neman kotu ta bayar da umarnin tsare su a ofishin hukumar EFCC kafin lokacin da za a saurari karar bayar da belinsu.

Mai shari’a Salihu ya daga shari’ar zuwa ranar Talata, 3 ga watan Yuli, domin sauraron bukatar bayar da belin wadanda ake tuhuma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel