Kotun musamman da aka kafa sun warware shari’a 324 a Najeriya

Kotun musamman da aka kafa sun warware shari’a 324 a Najeriya

Mun samu labari cewa a shekarar nan Kotun da aka kafa na musamman a zamanin Gwamnatin Buhari sun yanke hukunci fiye da 300 a cikin rabin shekara. Bayan nan kuma an dage wasu shari’an zuwa gaba.

Majalisar shari’a ta kasar watau NJC ta bayyana cewa Kotun da aka kafa sun zauna game da shari’a har 324 a cikin watanni 6. NJC tace ta kuma yi watsi da shari’a 12 ban da kuma wasu shari’a 62 da aka daga zuwa wani lokaci.

Kotun musamman da aka kafa sun warware shari’a 324 a Najeriya

An soma ganin amfanun Kotun musamman a Najeriya

Darektan yada labarai na Majalisar watau Soji Oye ya bayyana wannan a wani rahoto da ya gabatar game da binciken marasa gaskiya da satar dukiyar jama’a. Jaridar The Guardian ta kasar nan ce ta rahoto wannan a farkon makon nan.

KU KARANTA: 'Yan siyasa kadan ne za su iya ka da Buhari - Kwankwaso

Kotun kolin Najeriya ce ta yanke hukunci fiye da 50 daga cikin shari’ar da aka kai gaban ta. Bayan haka kuma Kotun kolin kasar ta dage shari’a 7 zuwa gaba. Kotun daukaka kara kuma ta zauna kan shari’a 74 kuma ta daga 11 zuwa gaba.

Babban Kotun Tarayya da ke Abuja kuma ya zauna kan shari'a 91 a wannan lokaci kamar yadda mu ka samu labari. A karshen shekarar bara ne dai aka kafa wadannan Kotu na musamman domin ganin bayan marasa gaskiya a kasar.

Jiya kun ki ji cewa manyan Jam’iyyun adawan kasar nan sun gama shirye-shiryen yadda za su tika Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kasa a zabe mai zuwa na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel