Nigerian news All categories All tags
Duba abinda wasu suka ji a jikin su kafin tankar mai ta fashe a Legas

Duba abinda wasu suka ji a jikin su kafin tankar mai ta fashe a Legas

Wata mata mai gashin masara wadda akafi sani da Mama Favour ta bayyana afkuwar wannan hatsari da mummanan abu, domin har yanzu bata farfado daga firgicin da ta shiga ba a sanadiyyar hakan, duk da cewa hatsarin ya afkune kwanaki 2 da suka gabata a ranar Alhamis

Duba abinda wasu suka ji a jikin su kafin tankar mai ta fashe a Legas

Duba abinda wasu suka ji a jikin su kafin tankar mai ta fashe a Legas

Wata mata mai gashin masara wadda akafi sani da Mama Favour ta bayyana afkuwar wannan hatsari da mummanan abu, domin har yanzu bata farfado daga firgicin da ta shiga ba a sanadiyyar hakan, duk da cewa hatsarin ya afkune kwanaki 2 da suka gabata a ranar Alhamis.

"Ina tsaye a wajen da nake gasa masara ta ina kokarin naga na saida masarar dana saro a kasuwa a safiyar ta Alhamis "

DUBA WANNAN: ITF zata dauki mutane 13,000 aiki

Mama Favour ta bayyana wa manema labarai cewa afkuwar hatsarin akwai wani abun mamaki a ciki domin kuwa yaronta daya tsallake rijiya da baya yana tare da ita a safiyar ranar ta Alhamis yabar wajen minti 10 kafin afkuwar hatsarin.

Tace "Dana yazo wajena a ranar ta Alhamis inda yake bayyana min cewa yanajin wani irin yanayi tattare dashi, yace jikinsa yana rawa sannan kansa yayi masa nauyi"

Ban maida hankali na a kansa ba har saida yacemin yana zaton wani abu zai faru a lokacin hankali na yanakan masara ta sannan lemata ta kare ni ya kira sunana da karfi yace Mama kalli kafin na dago kaina sai karar fashewar abu naji a take na fita da gudu saboda na rasa nutsuwa ta.

"Nayi gudu tun daga Otodela Bridge har zuwa Sakateriya ta Lagos sannan muka dakata, na manta da masara ta hade da waya ta a wajen"

Wani mai sana'a a wajen wanda bai bayyana sunan sa ba ya tofa albarkacin bakin sa inda yace

"Wannan abu ba abune na yau da kullum ba, duk ma wanda ya shiga rudu ya kamata ya dawo hankalin sa, ko yaushe munanan abubuwa sukan faru, tayaya zamu iya sanin cewa direban motar da kuma yaron mota zasu tsira ba tare da wani tabo ba sannan mutane da dama zasu rasa rayukan su?

Daya daga cikin manya manyan Priest Chief Ifayemi Elebuibon ya shawarci yan Nageriya dasu dinga tabbatar da lafiyar ababan hawansu kafin su dauki hanya sannan suma direbobin su dinga bin hanyar data dace.

Sannan yayi kira ga gwamnatoci dasu hana shigowar manyan motoci cikin gari sai da daddare don samun raguwar afkuwar hatsari a nan gaba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel