Nigerian news All categories All tags
Yanzu Yanzu: An dakatar da shugaban kungiyar kwallon kafa na Najeriya

Yanzu Yanzu: An dakatar da shugaban kungiyar kwallon kafa na Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bukaci Amaju Pinnick wadda ya kasance shugaban kungiyar kwalln kafa na Najeriyya (NFF) da ya sauka daga matsayinsa na shugaban kungiyar.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga ma’aikatar ci gaban mataa da wasanni karkashin ministan wasanni Solomon Dalung.

Sanarwar da ma’aikatar wasannin tayi ya nusar da umurnin babban kotun tarayya na ajiye zaben jami’an kungiyar na NFF wanda aka gudanar a ranar 30 ga watan Satumba a gefe wanda a zaben ne Amaju Pinnick ya zamo shugaban kungiyar.

Yanzu Yanzu: An dakatar da shugaban kungiyar kwallon kafa na Najeriya

Yanzu Yanzu: An dakatar da shugaban kungiyar kwallon kafa na Najeriya

Ministan wasanni Solomon Dalung ya fayyace yadda abun yake ta hannun hadimarsa Nneka Ikem Anibeze cewa babban alkalin alkalai na kasa kuma ministan shari’a ya umurce shi da ya dakatar da Amaju Pinnick daga nuna kansa a matsayin shugaban NFF.

KU KARANTA KUMA: An tsinci gawawwaki 23 a dajin Zamfara – Rahoto

Hakan ya ba Ambasada Chris Giwa damar zamowa shugaban kungiyar kwallon kafar na Najeriya (NFF).

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel