Nigerian news All categories All tags
Saraki da Tambuwal sun nemi a dakatar da shugabannin tsaro

Saraki da Tambuwal sun nemi a dakatar da shugabannin tsaro

Bayan yawan kashe-kashe dake karuwa a adin kasar, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto sun bukaci ayi gaggawan cire shugabannin tsaro domin a samu sabbin shawarwari kan yadda za’a kare kasar.

Tambuwal yayi Magana ne a taron kungiyar yan jarida wanda aka gudanar a Sokoto.

Gwamnan ya lura cewa babu amfanin ci gaba da rikon shugabannin tsaro da baza su iya kawo maslaha ga kalubalan tsaro a kasar ba.

Ya kuma bukaci kafofin watsa labarai da gwaneye da su daina wallafa labaran karya dake haddasa rikicin kabilanci da na addini a kasar.

A nashi bangaren, Saraki ya ce kashe-kashen da ake yi a fadin kasar ya wuce hankali saboda rayuka ake rasawa.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Bafarawa ya bayyana kudirinsa na takarar sugabancin kasa

Ya ga laifin shugabannin tsaro wajen rashin gudanar da aiki yadda ya kamata da kuma rashin ba majalisar dokoki hadin kai domin shawo kan matsalar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel