Nigerian news All categories All tags
Ka kashe kudin Abacha kan ayyukan da talakawa za su gani kuru-kuru da idanunsu – Shehu Sani ga Buhari

Ka kashe kudin Abacha kan ayyukan da talakawa za su gani kuru-kuru da idanunsu – Shehu Sani ga Buhari

Shehu Sani, sanatan dake wakiltan Kaduna ta tsakiya ya nuna rashin amincewarsa ga shirin gwamnatin tarayya kan yadda zata tafiyar da kudi dala miliyan 320 na Abacha wanda aka dawowa kasar da shi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za’a rarrabawa talakawan Najeriya kudin da aka maidowa kasar.

A ranar Juma’a, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa zata fara rabon kudin satan da aka dawo mata da su ga gidajen talakawa 302,000 a jihohi 19 a watan Yuli.

Ya yake sharhi akan lamarin ta shafinsa na twitter, sanatan yace kudin zai gare ne a hannun wadanda gwamnoni, ministoci, yan majalisa da mutanen Buhari suka bayar da sunayensu.

Ya bayyana cewa kawai a kashe kudaden wajen aiwatar da ayyukan da yan Najeriya za su gani da idanunsu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel