Ba batun zuwa Madrid: Salah ya tsawaita kwantiraginsa a kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool

Ba batun zuwa Madrid: Salah ya tsawaita kwantiraginsa a kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool

- Kwalelen Madrid da Barcelona don kuwa Salah ya sake rattaba hannu a Liverpool

- An sha hasashen cewa Salah zai sauya sheke a kakar wasanni mai zuwa

- Rattaba wannan kwantaragi na nufin Salah zai cigaba da zama a Liverpool har 2023

Mohammed Salah tare da kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool sun cimma yarjejeniya wajen sabunta kwantiraginsa, inda zai cigaba da zama a kungiyar har zuwa shekara ta 2023.

Ba batun zuwa Madrid: Salah ya tsawaita kwantiraginsa a kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool

Ba batun zuwa Madrid: Salah ya tsawaita kwantiraginsa a kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool

Kungiyar Liverpool ta yi hakan ne domin ta sakawa da Salah wajen nuna bajintar da yayi a kakar wasannin da ta gabata, wajen taimakawa kungiyar tasa zuwa gasar cin kofin zakarun Nahiyar turai tare da lashe kyautar gwarzon ɗan wasan da yafi kowa zura kwallaye a gasar premier ta kasar England.

KU KARANTA: Dan wasan gaba Ighalo ya nemi afuwar 'yan Nigeria kan wasan Argentina

Kungiyar ta sanar da wannan labari ne ta shafinta na intanet, inda aka nuna dan wasan tare da shugabannin kungiyar a yayin da yake rattaba hannun cimma yarjejeniyar.

Wannan yarjejeniya tasa Salah zai kasance dan wasa mafi daukar albashi da sauran kudade a cikin kungiyar.

Hakan ya biyo bayan ƙwazonsa da kungiyar ta yaba, wanda zai dinga ɗaukar kudi har miliyan £10 a duk shekara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel