Nigerian news All categories All tags
An matsawa shugaba Buhari kan cewa lallai sai ya salami shugabannin tsaro

An matsawa shugaba Buhari kan cewa lallai sai ya salami shugabannin tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na fuskantar matsin lamba kan cewa lallai sai dai ya salami shugabannin tsaronsa kan yawan kashe-kashe da ake fama da shi a fadin kasar.

A jiya wata kungiya mai rajjin ganin shugabanci nagari ta kai hart a nemi shugaban kasar yayi murabus. “Abun dake faruwa a yanzu zai zamo wasan yara idan har APC ta dawo mulki a 2019,” shugaban kungiyar, Nnosike Nwosu yayi gargadi.

Haka zalika Sata Dino Melaye na jihar Kogi ya goyi bayan wannan kira na dakatar da su. A wata sanarwa a Lokoja a jiya, ya zargi jami’an da rashin sanin makamin aiki sannan kuma cewa suna daburta lamaran kisan bayin Allah da ake yi, inda ya kara da cewa ya kamata shugabannin tsaro su jajirce kan aikinsu ko kuma su rasa matsayinsu.

An matsawa shugaba Buhari kan cewa lallai sai ya salami shugabannin tsaro

An matsawa shugaba Buhari kan cewa lallai sai ya salami shugabannin tsaro

Haka zalika cibiyar kare hakkin dan Adam ta kaddamar da kudirinta na kai shugaba Buhari kotun masu laifi na kasa-da-kasa kan rashin tsaro a kasar.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Bafarawa ya bayyana kudirinsa na takarar sugabancin kasa

Kungiyoyin jama’a da dama dai sun nuna goyon baya ga wannan kudiri na sallaman shugabannin tsaro, domin a ganinsu hakan zai kawo maslaha ga yawan kashe-kashe da ake fama da su a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel