Nigerian news All categories All tags
Sheke aya: Wanzami ya yiwa ‘yar shekara 6 fyade a Jihar Ogun

Sheke aya: Wanzami ya yiwa ‘yar shekara 6 fyade a Jihar Ogun

- Girma ya fadi rakumi ya shanye ruwan kaji inji masu iya magana

- Wani garjejen saurayi ne aka kama shi ya yiwa 'yar mitsilar yarinya fyade har sau uku

- Amma ya kekasa kasa ya ce shi ban san maganar ba, sai dai in ya san wata bai san wata ba

Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Ogun ta damke wani mai aski mai suna Daniel Essien mai kimanin shekaru 26 bisa zarginsa da yi wa wata kankanuwar yarinya fyade.

Sheke aya: Wanzami ya yiwa ‘yar shekara 6 fyade a Jihar Ogun

Sheke aya: Wanzami ya yiwa ‘yar shekara 6 fyade a Jihar Ogun

An dai bayyana yadda Daniel Essien ya yiwa kankanuwar yarinyar mai shekaru 6 fyade har sau 3 a unguwar Alagbole, Akute dake kan titin Olufemi Oshin.

Tun da farko dai yarinyar da aka yiwa fyaden ce ta shaidawa malaminta abin da ke faruwa, inda shi kuma nan take ya sanarwa da mahaifiyarta domin daukar mataki.

Jim kadan da samun wannan mummunan labarin sai mahaifiyar yarinyar ta garzaya ofishin ‘yan sanda domin sanar da jami'an tsaro.

KU KARANTA: Yan sanda sun cika hannunsu da wasu masu aika miyagun laifuka a jihar Legas

Wata sanarwa da kakakin rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar, ta bayyana yadda mahaifiyar yarinyar ta kai wannan bayani na yadda malamin yarinyar ya ce ya sanya idanu akan yarinyar, inda ita kuma daga nan ta kara lura sosai akan shige da ficenta.

Hakan ya ba ta nasarar ganin faruwar hakan bayan da yarinyar ta ke dawowa daga makaranta, shi kuma wannan mai askin yana kiranta domin cigaba da muguwar dabi'arsa.

Daga nan yan sanda su ka damke shi, da farko ya musanta faruwar al'amarin, amma ko da aka garzaya zuwa asibiti domin gudanar da bincike likita, sai ga shi sakamakon ya tabbatar da faruwar lamarin.

A karshe dai kwamishinan yan sandan jihar Ahmed Iliyasu ya bayar da umarnin cigaba da garkame Daniel din domin cigaba da bincike

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel