Nigerian news All categories All tags
Akwai bukatar mu sake fasalin hukumomin tsaron Najeriya – Makarfi

Akwai bukatar mu sake fasalin hukumomin tsaron Najeriya – Makarfi

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi ya ce babu laifi don an sake fasalin lamuran Najeriya idan dai har an sabawa ginshikin hakan.

Dan takarar shugaban kasar karkashin lemar PDP yace akwai bukatar sabonta lamuran hukumomin gwamnati wadanda suka hada da hukumomin tsaro domin bautawaa yan Najeriya ba wai shugabanni ba.

Akwai bukatar mu sake fasalin hukumomin tsaron Najeriya – Makarfi

Akwai bukatar mu sake fasalin hukumomin tsaron Najeriya – Makarfi

Makarfi wanda yayi Magana a zauren kungiyar tsoffin dalibai na Unity Schools Old Students Association, USOSA, inda ya bayar da darasi kan ‘zaman lafiya da hadin kai: a jihar Rivers ya ce “yadda hukumomin Najeriya ke tafiyar da hukumominsu a yanzu, suna yi ne domin san ran shugabanni ba wai al’umman kasa ba."

A halin da ake ciki, rikicin cikin gida ya sake tunkaro jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna, yayinda manyan mambobin jam’iyyar ke sake sauya sheka daga jam’iyyar.

Hakan ya biyo bayan zargin da suke yi na cewa masu tafiyar da jam’iyyar a jihar basu da kwarewa.

KU KARANTA KUMA: Ango Abdullahi ya hadu da Obasanjo kan zaben 2019 da kashe-kashe

Yan kwanaki kadan baya, wani tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar, Isa Ashiru Kudan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) sannan a yanzu wani babban jigon jam’iyyar a jihar, Alhaji Lawal Adamu Usman, wanda aka fi sani da Mr LA ya yi murabus.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel