Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Daga karshe, Kotu ta baiwa Kanal Sambo Dasuki beli

Yanzu-yanzu: Daga karshe, Kotu ta baiwa Kanal Sambo Dasuki beli

Labarin da ke shigowa da dumi-dumi na nuna cewa babban kotun tarayya da ke zaune a birnin tarayya Abuja ta baiwa tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki, beli.

Hukumar DSS ta kasance tana rike da Dasuki ne tun shekarar 2015 duk da cewa kotuna daban-daban sun basa beli.

Alkali mai shari'a ya bada belin Dasuki a yau Litinin, 2 ga watan Yuli 2018 kan kudi N200 million da kuma wadanda za su tsaya masa.

Alkalin ya ce wadanda zasu tsaya wajibi ne su kasance wadanda suka kai matsayin dirakta a aikin gwamnati. Idan marasa aikin gwamnati ne, su kasance masu dukiya a birnin tarayya Abuja.

Yanzu-yanzu: Daga karshe, Kotu ta baiwa Kanal Sambo Dasuki beli

Yanzu-yanzu: Daga karshe, Kotu ta baiwa Kanal Sambo Dasuki beli

Hukumar DSS ta damke kanal Sambo Dasuki ne bisa ga karkatar da makudan kudi da aka bada domin sayan makami don yakan mayakan Boko Haram lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

KU KARANTA: Bayan kashe mutane 10 tare Sojoji sun damke wasu mahara a jihar Filato

Binciken hukumar EFCC ya nuna cewa a maimakon siyan makamai a lokacin, tsohon NSA Sambo Dasuki ya kasance ya raba kudaden ga makusantansa domin wani manufa daban.

Daga cikin wadanda suka amfana da wannan kudi sune tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, wanda ya amshi N2bn domin addu'an cin zabe; shugaba gidan talabjin AIT, Raymond Dokpesi, wanda ya amshi akalla N2bn domin yada farfaganda.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel