Nigerian news All categories All tags
Martanin hukumar zabe (INEC) kan masu yunkurin yin siyarwa da mutane katin zabe

Martanin hukumar zabe (INEC) kan masu yunkurin yin siyarwa da mutane katin zabe

- INEC ta yi shirin dakile kokarin 'yan damfara masu shirin siyarwa da mutane katin zabe na jabu

- Kuma hukumar zaben ta ce ko a baya ma an gwada katin bogin bai yi aiki a na'urarta ba

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta samu rahotan yunkurin da wasu su ke yi na samar da katin zabe na jabu domin sayar da shi ta kafar intanet.

Martanin hukumar zabe (INEC) kan masu yunkurin yin siyarwa da mutane katin zabe

Martanin hukumar zabe (INEC) kan masu yunkurin yin siyarwa da mutane katin zabe

Wannan jawabin ya fitowa ne daga bakin daraktan wayar da kai akan harkokin katin shaidar zabe Oluwole Osaze Uzzi cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar ta INEC ta dauki dukkanin wani mataki na ganin hakar su bai cimma ruwa ba. Domin INEC ta samar da ingantattun lambobin sirri ga katunan zaben da wanda hakan zai kare su daga Dukkanin wata barazana.

KU KARANTA: Zaɓen jihar Ekiti: Hukumar zaɓe ta ƙasa ba ta raba kayan aiki a wasu ƙananan hukumomi ba

A karshe sanarwar ta bukaci mutane da su kauracewa irin wadannan jita-jitar dillalan ‘yan damfarar.

Sannan kuma Jama'a su bayar da hadin kai wajen wayar da kan al'umma akan yunkurin da wasu su ke na samar da katin zaben na Jabu.

Ya kuma tabbatar da cewa na'urar tantance katin zabe ba za ta taba tantace katin da ya ke na jabu ba, sabo da ingancinta. Domin kuwa har an tabbatar da hakan a jihohin Osun da Ekiti.

Ya kuma kara jaddada cewa har yanzu matsayin hukumar zabe na tabbatar da sahihin zabe a kasar nan yana nan daram.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel